News

BIDIYO: Yadda Ake Dauko Gawarwakin Mutum Goma Sha Biyar 15 Din Da Suka Nutse A Kogin Maiduguri

BIDIYO: Yadda Ake Dauko Gawarwakin Mutum Goma Sha Biyar 15 Din Da Suka Nutse A Kogin Maiduguri

Akalla gawarwakin mutum 15 aka gano a kogin Ngadabul a Maiduguri, babban birnin jihar Borno bayan afkuwar wata ambaliya.

Kodinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA a arewa maso gabas, Muhammad Usman, shi ya bayyana hakan a jiya Laraba, yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a Maiduguri.

Usman ya ce ana samun karuwar mutane da ke nutsewa cikin kogin sakamakon ambaliya wanda kuma ya shafi al’ummomi da ke kusa bakin kogin a Maiduguri.

Ya bukaci iyaye da su gargadi ‘ya’yansu kan yin ninkaya a kogin domin kaucewa nutsewa.

Kodinetan na NEMA ya kara da cewa hukumar ta samar da kayakin gagaji da za ta baiwa wadanda ambaliyar ta shafa inda kuma take wayar da kan al’umma kan haduran ambaliyar ruwa da kuma hanyoyi da za su kare kansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button