News

Innalillahiwainnailaihiraju’un.! Bidiyon Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Shafe Gidaje Da Motoci A Garin Kontagora

Innalillahiwainnailaihiraju’un.! Bidiyon Yadda Ambaliyar Ruwa Ta Shafe Gidaje Da Motoci A Garin Kontagora

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu Yanzu Daga Zakari Y. Adamu, Kontagora Na Cewa.

Mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka samu a ranar laraba a garin kwantagora ya haddasa mummunar barna.

 

Mamakon ambaliyar ruwa ya shafe gidaje da motoci da sauran ƙaddarori a garin Kontagora dake Jihar Neja, sakamakon ruwan sama da aka yi kamar da bakin ƙwarya a garin na Kontagora da kewaye a jiya Laraba.

Unguwannin da wannan al’amari ya shafa dai sun haɗa da, BCJA, Gangaren Sabon Gari, Unguwan Tukura da Gangaren Mayanka/Unguwan Yamma.

Sakamakon wannan mamakon ruwa ya haddasa asarar dumbin dukiya tare da shafe gidaje Da motoci.

Anan muke addu’ar Allah Ya Mayarwa wadanda suka rasa dukiyar su da Alkhairi

Ga Cikakken Rahoton.

https://youtu.be/KFuP4ZRXnBw

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button