News

BIDIYO: Yadda Mahaifiyar Hanifah Ta Nannaushi Malamin Da Yai Garkuwa Da Kashe ƴar Ta a Kano

Yadda mahaifiyar Hanifah ta nannaushi malamin da yai garkuwa da kashe ƴar ta a Kano

Mahaifiyar Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5 da malamin makarantar su Noble Kids Academy, Abdulmalik Tanko, ta fusata ta nannaushe shi bayan da ƴan sanda su ka kawo shi Shalkwatar Ƴan Sanda a Kano.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Laraba ne dai dubun Tanko ta cika, bayan da ya ɗauke Hanifah tsawon sama da kwanaki 40, inda da ga bisani ya kashe ta bayan ya karɓi wani abu daga cikin naira miliyan 6 da ya ce a bashi kuɗin fansa.

A yau Juma’a ne Rundunar Ƴan Sanda ta yi holon Tanko da sauran waɗanda ake zargi da hannu a kashe yarinyar.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa su ma iyayen marigayiya Hanifah sun zo shelkwatar ƴan sandan.

Jaridar ta ce iyayen Hanifah ne su ka fara zuwa wajenz inda da ga bisani sai a ka kawo Tanko da sauran waɗanda a ke zargi.

Da ga zuwan masu laifin, sai mahaifiyar Hanifah, Fatima Maina, ta hango Tanko, in da ta yi kansa, ta cakumo shi, sannan ta riƙa zabga masa mari da naushi.

Lamarin ya sanya ƴan sanda su ka zaburar su ka ɗauke Tanko ɗin, inda saura kuma su ka riƙa baiwa Fatima haƙuri.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button