News

BIDIYO: Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutum Dari Da Talatin 130 A Jihar Filato

BIDIYO: Yan Bindiga Sun Kashe Fiye Da Mutum Dari Da Talatin 130 A Jihar Filato

Mutane da dama sun mutu yayin da ƴan ta’adda su ka kai hari a ƙauyuka 4 a Plateau.

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin ƴan fashin daji ne sun kai hari tare da kashe mutane, gani da ƙona gidaje da dama a wasu ƙauyuka hudu na Ƙaramar Hukumar Kanam da ke Jihar Plateau.

Maharan sun kai farmaki kauyukan ne da yammacin jiya Lahadi, inda suka yi ta harbe-harbe tare da kona kadarori na mutanen yankin.

Wani mazaunin yankin, Danladi Dukup, ya shaida wa NAN cewa wasu mutanen sun rasa rayukansu yayin da wasu su ka samu raunuka daban-daban.

Ya ce da yawa daga cikin mutanen kauyen sun gudu daga gidajensu domin tsira da rayukansu bayan an kawo harin.

Maj. Ishaku Takwa, jami’in yada labarai na Operation Safe Haven (OPSH), rundunar soji da ke wanzar da zaman lafiya a Plateau da kewaye, ya tabbatar wa manema labarai harin a jiya Lahadi a Jos.

Takwa, wanda bai tabbatar da adadin mutanen da su ka mutu ko kuma suka jikkata ba, amma dai ya ce an tura dakarun rundunar zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya.

Wannan harin na zuwa ne sa’o’i 24 da sace mata da ‘yar Kwamishinan Muhalli na jihar.

https://youtu.be/eAt6cFp6hlw

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button