News

BIDIYO: ‘Yan IPOB Sun Kashe Wata Mace Mai Ciki Da Yaranta 4 Da Karin Wasu ‘Yan Arewa 6 a Anambra

BIDIYO: ‘Yan IPOB Sun Kashe Wata Mace Mai Ciki Da Yaranta 4 Da Wasu Karin Wasu ‘Yan Arewa 6 a Anambra

Kamar Yadda Zaku Kalla A Bidiyon, Zakuga Yadda Mayakan IPOB a ranar Lahadi suka halaka wata mata Mak Ciki da yaranta 4 da kuma wasu mutane 6, duk ‘yan arewa a Jihar Anambra.

 

Sun halaka matar wacce ta ke dauke da juna-biyu a Isulo, cikin karamar hukumar Orumba ta arewa da ke jihar ba tare da ta yi musu komai ba.

Sarkin Hausawan yankin, Alhaji Sa’id Muhammad a jiya ya koka inda ya ce ‘yan arewa da ke zama a jihar sun yanke shawarar tserewa.

Sai dai bayan sa’o’i 48 da kashe-kashen ranar Lahadi wanda aka dinga halaka ‘yan arewa ba tare da sun yi komai ba, babu wata jarida ko gidan talabijin da su ka wallafa labarin duk da yadda hotunan su ka bazu a kafafen sada zumunta da kuma caccakar da jami’an tsaro, kungiyoyi da mutane su ka dinga yi.

Kashe-kashen ‘yan arewan da kungiyar, mai keta dokoki ta yi ya auku ne bayan kwanaki kadan da bayyanar dan majalisar Jihar Anambra wanda ‘yan ta’adda su ka sace.

“Matar asali ‘yar Jihar Adamawa ce. Kafin rasuwarta, ta zauna a Orumba ta Kudu ne kuma a ranar Lahadi ta je kai wa wasu kawayenta ziyara ne tare da yaranta hudu.

“A hanyarta ta komawa gida aka halaka ta. An daukota a babur din haya, daga nan ‘yan bindigan su ka kai musu farmaki, su ka halaka ta da yaranta hudu yayin da mai babur din ya tsere.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button