News

BIDIYO: Zamfara: ‘Yan sanda sun kama masu ci da sayar da naman mutane A Zamfara.

Zamfara: ‘Yan sanda sun kama masu ci da sayar da naman mutane A Zamfara.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya a jihar Zamfara da ke arewa maso yammaci ta kama mutum hudu da zargin ci da kuma sayar da sassan jikin dan adam, wani abu da ba a saba gani ba a jihar.

A taron manema labarai da ya gudanar a Gusau babban birnin jihar ta Zamfara ranar Alhamis, Kwamishinan ‘yan sanda Ayuba Elkana ya ce an damke wadanda ake zargin ne bayan da jami’an tsaro suka tsinci gawa a wani kango, ba tare da wasu sassan jikinta ba.

Gano gawar wani bangare ne na bincike da ake yi kan batan wani yaro dan shekara tara.

Tun a makon da ya gabata aka ma mutanen hudu da a ke zargi, da suka hada da wasu magidanta maza biyu da kuma matasa suma maza biyu kamar yadda CP Elkana ya sanar.

Ya kara da cewa yanzu haka ana kan neman wasu mambobin kungiyar da ake zargi da cin naman mutane.

Kazalika kwamishinan ‘yan sandan ya ce kawo yanzu bincike ya nuna cewa sau biyu shugaban kungiyar na tura wa uku daga cikin wadanda aka kama naira 500,000 na cinikin sassan jikin dan adam.

Cin nama da sayar da sassan jikin mutane wani sabon abu ne a Zamfara, duk da jihar ta yi kaurin suna wurin kashe-kashe da garkuwa da mutane don neman kudin fansa daga ‘yan bindiga tsawon shekaru.

Kuma hukumomin Najeriya na shan suka saboda nuna gazawa wurin shawo kan halin da jihar ke ciki.

A wata mai kama da haka yayin zantawa da manema labaran CP Ayuba Elkana ya ce jam’ian tsaro sun kubutar da mutun 17 da aka sato daga jihar Neja aka shiga da su Zamfara.

Ya kara da cewa yayin wani sintiri, ‘yan sanda sun kwato makamai da suka hada da bindigar harba makamin roka, bayan bata kashi da ‘yan bindiga a wani daji da ke yankin.

A makon da ya gabata ne ‘yan fashin daji suka kashe kusan mutun 200, a lokacin da suka kai wasu jerin hare-hare a kauyukan kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.

https://youtu.be/2X-HECgzb58

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button