News

Yayiwa Yar Shekara Uku Fyade Anguwar Doya dake cikin garin Kirfi a jihar Bauchi, Daga Datti Assalafy

YA YIWA ‘YAR SHEKARA 3 FYADE

Wannan mutumi da kuke gani a hoto sunansa Ali Lawan yana da zama a Anguwar Doya dake cikin garin Kirfi a jihar Bauchi, ya auri wata mata a matsayin bazawara, tazo gidansa da karamar yarinya ‘yar shekara uku

Kwanaki biyar da suka wuce, wato ranar Lahadi 9-1-2022 da misalin karfe 6 na yammaci, sai Ali Lawan ya bukaci matarsa ta kawo masa taburma zai kwantar da ‘yar matar nasa

Bayan ta kawomasa taburma ya kwantar da yarinyar kuma matar ta bar gurin, zuwa wani lokaci da ta dawo sai ta tarar da ‘yarta cikin mawuyancin hali tana amai ta baki da hanci, da ta duba gaban yarinyar sai ta ga ya dagargaje yana ta zubar da jini

Nan take matar ta garzaya ofishin ‘yan sanda na karamar hukumar Kirfi, ‘yan sanda suka zo suka kama mijinta Ali, an kai yarinyar ‘yar shekara uku zuwa Asibiti inda Likitoci suka tabbatar Ali ya yiwa yarinyar fyade

Yanzu haka Ali yana sashin binciken manyan laifuka na rundinar ‘yan sandan jihar Bauchi wato State CIID, bayan kammala bincike za’a mikashi zuwa kotu

Allah Ya sauwake

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button