News

Bidiyon Yadda Ɓarayin Daji Sukayi Yunƙurin Shiga Wani Gida A Funtua Jahar Katsina

Bidiyon Yadda Ɓarayin Daji Sukayi Yunƙurin Shiga Wani Gida A Funtua…

Lamarin ɓarayin daji yana ƙara ta’azzara a jihar Katsina kamar yadda zaku gani a cikin wannan bidiyo, daren ranar Juma’ar da ta gabata ne 02/09/2022 da misalin ƙarfe 10:20 na Dare masu garkuwa da mutane suka shiga gidan wani Electrical Engineer a garin Funtua jihar Katsina, kamar yadda wakilin jaridar Amintacciya ya rawaito.

Allah cikin Ikonshi ya sa mutumin baya gida tare da iyalansa, masu gadin gidan kuma da suka lura da zuwan Ɓarayin sun gudu domin tsira da rayukan su, ƴan ta’adar sun samu nasaran karya kofar shiga Gidan ta farko wato gate suka shiga gidan, amma basu iya balle kofar shiga cikin falo da dakunan gidan ba.

Shi kuma Mai gidan ya kafa CCTV Camera suna Naɗar faifan bidiyo na duk abinda yake faruwa a gidansa ko da baya nan, da yake masani ne na Na’urori ya haɗa CCTV Camera ɗin da wayar shi ta salula.

Kasancewar Alla bai basu ikon shiga Gidan ba, hakan yasa suka fita daga gidan, suka shiga wata unguwa da ake kira Project Quarters Funtua suka ƙwashi mutane da yawa suka tafi dasu Daji, wannan yanayin dai shike ta faruwa a Ɗan tsakanin nan a ƙananan Hukumomin Bakori da Funtua.

Al’amarin nan dai abu ne mai Matuƙar tada hankali, ko a satin da ya gabata Ƴan Ta’adar Nan sun sakama wata Motar sulke ta Jami’an tsaro wani abun fashewa a ƙaramar hukumar Jibia Lamarin da yayi sanadiyyar rasa rayukan wasu Jami’an tsaro tare da jiggata wasu, amma ganin yadda Gwamnati ta sayo Motocin sulke domin tunkarar Lamarin hakan yana Ɗan sanyaya zukatan Al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button