News

Bidiyon Yadda Aka Kama Azzalumin Da Ya Kwakwalewa Wani Yaro Idanu A Jihar Bauchi Har Ya Shiga Hannu

Innalillahi Azzalumin Da Ya Kwakwalewa Wani Yaro Idanu A Jihar Bauchi Ya Shiga Hannu

Azzalumin Da Ya Kwakwalewa Wani Yaro Idanu A Jihar Bauchi Ya Shiga Hannu

Idan jama’a basu manta ba, kwanaki biyu da suka wuce na kawo labarin wani yaro matashi Uzairu Salisu a cikin garin Bauchi wanda wani bakin azzalumi matsafi mai suna Ibrahim ya yaudareshi da niyyar zai bashi kwadago ya kaishi gonarsa ya daureshi ya kwakwule masa idanu guda biyu ya gudu da su.

Bisa taimakon Allah ‘yan sanda sunyi kokarin bin diddigin Ibrahim suka kamashi tare da kwayar idanun Uzairu guda biyu da ya cire kamar yadda zaku gani a hoto

Uzairu ya fara samun sauki sakamakon kula da lafiyarsa da ake a Asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital Bauchi

Allah Ka kare mu daga sharrin azzalumai matsafa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button