News

BIDIYO:Yan kungiyar Ansaru sun fara bawa sababbin membobin su kayan sawa na bai daya.

BIDIYO:Yan kungiyar Ansaru sun fara bawa sababbin membobin su kayan sawa na bai daya.

Wani rahoto na cewa, yan kungiyar ansaru sun fara baiwa sabbin mambobin su kaya na bai daya.

Rahoton da ya fito daga Aliyu samba wanda ya wallafa cewa ana baiwa sabbin mambobin kayan ne a garuruwan Makera, Birnin Gwari, Dogon Dawa, Damari da kuma Shado.

Rahotanni sun bayyana cewar sun fara basu kayan ne domin su banbanta mambobinsu da sauran ‘yan bindiga da kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke zuwa yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Ko A Baya Bayan nan dai saida Kungiyar tai ikirarin kawo cikasa a zabukan da za’a gudanar a jahar kaduna.

Kungiyar ansaru ta dade tana ayyukan ta’addanci da kashe kashe a yankin arewa.

📷 Twitter/ Edress4P

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button