Politics

DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Umarci Sufeton ‘Yansanda Ya Kama Bola Tinubu

DA DUMI-DUMI: Kotu Ta Umarci Sufeton ‘Yansanda Ya Kama Bola Tinubu

Wata Babbar Kotun taraiyya dake zamanta a Abuja, ta sahhalewa wata kungiyar farar hula samun wani umarnin kotu dake neman tursasa Sufeton Yansanda na kasa, gurfanar da Dantakarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC Bola Tinubu bisa zarginsa da bada bayanan Karya.

Da yake yanke hukunci, Mai shari’a Inyang Ekwo ya amince da bukatar kungiyar mai suna CRPA a takaice, ta karkashin lauyanta Ugo Nwofor.

Karar da kungiyar ta kai Kotu, Ya biyo bayan kin amincewar da Sufeton Yansanda na kasa Usman Alkali Baba yayi , na kin gurfanar da tsohon gwamnan jihar legas din a gaban kotu, bisa zarginsa da bada bayanan karya akan takardun shaidar kammala karatunsa.

Alkalin kotun yace, bukatar kungiyar tana bisa bisa ka’ida, kuma bata sabawa wata doka ba, daga nan ne y adage cigaba da zaman shari’ar zuwa ranar 1 ga watan Nuwambar Bana domin sauraren cikakkiyar shari’ar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button