News

CIKIN BIDIYO: Jam’iyyar Adawa Ta PDP Ta Gargadi Ganduje Kada Ya Tatsi Kudi Kan Sabunta Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu A Kano

Babban Jam’iyyar Adawa Ta PDP Dake Jahar Kano Tayi Kira Da Gwamnan Jahar Abdullahi Umar Ganduje.

Da Kada Yayi Amfani Da Soke Lasisin Makarantu Masu Zaman Kansu Wajen Tatsar Kudade Daga Masu Makarantun.

Kamar Yadda Zaku Gani Cikin Wannan Bidiyon Dake Kasa,

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta na jahar wato shehu wada sagagi, inda acikin wasikar suke nuna alhinin rashin yarinyar nan mai shekaru 5 hanifa abubakar wadda ta rasa ranta a hannun shugaban makarantar su da ya saceta, tare da neman kudin fansa daga iyayen ta.

Haka zalika jam’iyyar ta PDP ta jinjinawa jami’an tsaro bisa namijin kokarin da sukai na saurin gano makasan tare da turo su kotu.

Jam’iyyar ta bukaci gwamnatin jihar karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje da ta bi ka’idojin da doka ta gindaya na sanya ido tare da gudanar da makarantu masu zaman kansu wajen aiwatar da gyare-gyaren.

Ga Bidiyon Nan 👇👇 Asha Kallo Lafiya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button