News

Gwamna Ganduje Yasha Alwashin Da Zarar Kotu Da Yanke Hukuncin Kisa Akan Wanda Ya Kashe Hanifa To Bazai Bata Lokacin Saka Hannu Ba

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Yakai Ziyara Gidan Su Marigayi Hanifa Abubakar.

Kuma Gwamna Ganduje Yayi Alkawarin Kula Da Iyayen Marigaya Hanifa.

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Yakai Ziyarar Ta’aziya Ga Iyayen Hanifa Abubakar Wadda Ta Rasa Ranta A Hannun Malaminta Da Yai Garkuwa Da Ita.

Kwana 47 bayan ya sace dalibar tasa mai shekaru biyar a duniya, jami’an tsaro sunyi nasarar kama Abdulmalik Tanko a lokacin da ya je karbar kudin fansar hanifa.

Amma gabanin hakan malamin makarantar ta Noble Kids Academy, ya riga ya kashe Hanifa amma duk da haka yake karbar kudin fansa a hannun iyayen hanifar.

“Mun samu tabbaci daga kotun da ke sauraren karar cewa za a yi adalci.”a cewar Ganduje yayin ziyarar ta’aziyyar kamar yadda Sakataren yada labaransa Abba Anwar ya sanar a ranar Litinin.

Hakazalika Gwamna Ganduje yasha alwashin ba zai wani bata lokaci ba wajen bin umarnin kotu da zarar an yanke hukuncin kisa.

“Duk wanda aka samu da laifi a wannan mummunan aika-aika, zai fuskanci hukuncin kisa ba tare da bata lokaci ba, a matsayinmu na gwamnati, tuni mun riga mun fara bin matakan da suka dace.”

Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta kula da iyayen marigayiya Hanifa.

Gwamna Ganduje ya kuma yi alkawarin cewa gwamnati za ta kula da iyayen marigayiya Hanifa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button