News

CIKIN BIDIYO: Yadda Aka Tasa Keyar Makasan Hanifa Abubakar Izuwa Gidan Gyaran Hali

Kotu ta tisa ƙeyar makasan Hanifah zuwa gidan gyaran hali.

Daga Aliyu Samba

Kamar Yadda Zaku Gani Acikin Bidiyon An gurfanar da Abdulmalik Muhammad Tanko, Hashim Isyaku da Fatima Jibrin Musa a gaban kotun Majistrate dake zaman ta gidan Murtala a jihar Kano.

An gurfanar da wadanda ake zargin ne da aikata laifukan hada kai don aikata laifi, garkuwa, biye wanda akai garkuwa da shi da laifin kisan kai.

M.A LAWAN Kwamishinan Shari’a na jihar Kano shine ya gabatar da ƙara a gaban mai Shari’a Mohammed Jibrin da misalin karfe 2:40 na yamma, inda ya bayyanawa kotu cewa nan da kwana 7 zasu gurfanar da wadanda ake ƙara a gaban kotun da take da hurumi da irin laifin su.

Bayan gabatar da wadanda ake ƙara a gaban kotu, an karanta musu tuhumar da ake yi musu cikin harshen turanci, inda aka fassara cikin harshen Hausa:

” Ana tuhumar ku da laifin hada kai don aikata laifi, garkuwa, boye wanda akai garkuwa da shi da laifin kisan kai”

”kai Abdulmalik Mohammed Tanko Mai shekaru 34, malamin makaranta mai makarantar Noble kids dake Kwanar dakata a karamar hukumar Nassarawa a jihar Kano, ka haɗa kai da Hashimu Isyaku mai shekaru 37 da Fatima Jibrin mai shekaru 26 dukkan ku yan unguwar Tudun Murtala dake Kano, kuka aikata laifin garkuwa da Hanifah Abubakar yar shekara 5, tare da ɓoye ta a inda kuka yi garkuwa da ita, ku ka kuma kashe ta, wacca ɗaliba ce a makarantar ka, kuka ci zarafin ta, kuka cutar da ita, kuka boye ta.”

”Sannan kai Abdulmalik ka kashe Hanifa Abubakar da shinkafar bera, ka gutsutsura sassan jikin ta, ka sa a ta buhu.”

”kai kuma Hashimu ka binne ta a wani kabari dan kankani a makaranta Noble Kids, kafin ku karbi ₦100,000 a hannun iyayen ta cikin ₦6,000,000 da kuka ce a baku kuɗin fansa” Inji wani sashe na tuhumar.

Mai gabatar da ƙarar ya shedawa kotu cewa Ƴan sanda sun kammala bincike, kuma wadanda ake tuhuma sun fahimci tuhumar a ake musu, sakamakon haka, sun rokon kotu data bada umarnin tsare wadanda ake tuhuma su 3 duba da irin girman laifin da ake tuhumar su dashi.

Sunyi alkawarin zasu gurfanar dasu a gaban kotun da zatayi Shari’ar su cikin kwana 7 kacal.

Mai Shari’a Mohammed Jibrin ya bada umarnin kaishi gidan gyaran hali, ya kuma daga zaman zuwa 2/2/2022 domin a cigaba da saurare.

https://youtu.be/WwlOvi6UYzk

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button