Cikin Bidiyo: Yan Biafra Sun Fille Kan Wasu Muslmai Biyu Yan Arewa
Cikin Wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna Yadda Mambobin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, Wato IPOB suke baje kolin kawunan musulmin Arewa guda biyu da suka kashe.
Bayan Gama Fille Kawunan Nasu Ne, daya ya tsuguna a kusa da Kan Da Ya Fille Sannan Ya bude wuta, an ga maharan dauke da makamai suna murna da farin ciki tare da bayyana hanci da goshin daya daga cikin wadanda abin ya shafa a matsayin “Hausa”.
Daya daga cikin masu tayar da kayar bayan yana rera taken yaki yana murzawa daya daga cikin kawunan biyu, daya daga cikin maharan ya ce da harshen Igbo, “Wannan Bahaushe ne yanzu”, yayin da wani kuma ya ce shi Bafulatani ne.
Bidiyon ya kuma nuna daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su da aka yi wa kawanya, wanda ake kyautata zaton shi ne ubangidan mutanen biyu da aka yanke, zaune da kafafunsa da igiya.
Wani kwararre kan harkokin tsaro da ya yi nazari a kan faifan bidiyon ga jarida https://dailynigerian.com/ ya tabbatar da sahihancin sa, inda ya ce lamarin ya faru kwanan nan.