News

DA ƊUMI-ƊUMI: Matasa sun bābbake shaguna da gidāje da dama a garin Warji jihar Bauchi bayan wata ma’aikaciyar ƙaramar hukumar ta yi kalaman ɓatānci ga Annabi SAW.

DA ƊUMI-ƊUMI: Matasa sun bābbake shaguna da gidāje da dama a garin Warji jihar Bauchi bayan wata ma’aikaciyar ƙaramar hukumar ta yi kalaman ɓatānci ga Annabi SAW.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Bauchi Ahmed Wakil ya bayyana cewa an babake gidaje shida da shaguna 7 a rikicin.

Majiya ta shaida cewa wata mata mai shekaru 40 Rhoda Jatau ta saka kalaman ɓatanci ga Annabi SAW yanar gizo da hakan ya ingiza matasa.

Wannan abu da tayi ya tunzura matasa musulmai da ya kaiga han yi waɗannan kone kone a karamar hukumar.

Rhoda ma’aikaciyar karamar Hukumar Warji ne dake jihar Bauchi.

Rundunar ƴan sanda sun yi kira ga matasa da su kwantar da hankalin su cewa jami’an tsaro na yin bincike akai.

Sannan kuma kwamishinan ƴan sandan jihar shima ya roki iyaye, Malaman addini da shugabannin alumma da su ja wa ƴaƴan su kunne su daina aikata abinda zao tada zaune tsaye a kasar nan.

– Premium Times Hausa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button