Religion

Wani limamin coci, Fasto Akintaro Joshua Ojo, ya yi batanci ga Allah da Annabi Muhammad (SAW) da Al-Kur’ani.

Wani Fasto Ya Yi Batanci Ga Annabi Muhammad (SAW) Da Al-Kura’ni

Wani limamin coci, Fasto Akintaro Joshua Ojo, ya yi batanci ga Allah da Annabi Muhammad (SAW) da Al-Kur’ani.

A ranar Asabar, Kungiyar Kare Hakki ta Musulmi (MURIC) ta bukaci mahukunta su tsare Fasto Akintaro wanda ya saki wani bidiyo, yana batanci ga Allah (SWT) da Al-Kur’ani da Annabi Muhammad (SAW) da kuma addinin Islama.

MURIC ta ce faston ya yi barambaramar ce a lokacin da yake ta’aziyya kan rasuwar Deborah Samuel, dalibar da ake zargin an kashe saboda ta yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar Sakkwato.

Kimanin mako biyu ke nan da aka hallaka Deborah, dalibar Kwalejin Ilimi na Shehu Shagari da ke Jihar Sakkwato, kan yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW), lamarin da ya haifar ta tashin hankali sosai.

Shugaban Kungiyar MURIC Reshen Jihar Osun, Dokta Abdulazeez Ademokoya, ya bayyana abin da Faston ya ce batancin da fasto ya yi ya ninka katobarar Deborah Samuel.


MURIC ta bayyana cewa babu wani Musulmi mai lafiyayyen hankali da zai lamunci kalaman faston, wadanda za su iya jefa Jihar Osun da daukacin Yankin Kudu maso Yamma a cikin tashin hankali ko rikicin addini.

Kalaman batancin da MURIC ta nakalto faston ya furta sun yi tsananin muni da Aminiya ba za ta iya rubutawa.

Baya ga haka, an ji faston yana kore samuwar Allah da tsarkinSa, da kuma samuwar Mala’ika Jibril.

Bugu da kari, har ya ba da lambobin wayarsa, da cewa a shirye yake da duk mai neman far mishi.

Amma kungiyar ta ce “Ba za mu dauki doka a hannunmu ba, muna kuma kira ga daukacin Musulmin Jihar Osun su bari hukumomin tsaro su yi abin da ya dace a kan lamarin.

“Yankin Kudu maso Yamma ya fi kowane yankin Najeriya hadari, saboda yawan Musulmi da Kiristoci da mabiya wasu addinai, domin haka duk rikicin addinin da aka samu a yankin na iya sanadin asarar miliyoyin rayuka,” a cewar Dokta Ademokoya.

Kungiyar ta bayyana mamakin hadafin Fasto Akintaro a yankin Kudu maso Yamma, da irin miyagun kalaman da ya furta ga Allah da Manzon Allah (SAW) da Al-Kur’ani ba.

“Ya yi ne domin tunzura Musulmi su far wa Kiristoci? So yake ya tunzura mutane su yi gaban kansu? Ko kuma so yake ya kawo matsala ga zbaen da ke tare a Jihar Osun?

“Ba mamaki kuma ya yi ne domin ya kawo cikas ga harkokin hadahadar jama’a a harkokin addini.

“Ko kuma ya yi ne domin haddasa lalata dukiyar al’umma da haddasa rikicin addini? Ya kamata ya fito ya amsa waddanann tambayoyin.

“MURIC reshen Jihar Osun na kira ga al’ummar Musulmi da su kwantar da hankulansu a jihar. Don Allah kar ku yi gaban kanku, ku kasance masu bin doka.

“Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun da sauran hukumomin tsaro kuma muna rokon su, da su gaggauta daukar matakin da ya dace, domin kauce wa wani sabon tashin hankali da ke iya jan asarar rayuka a yankin Kudu maso Yamma,” kamar yadda ya bayyana.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button