News

Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

Yan Arewa Masu Kai Abinci Yankin Inyamurai Su Dakatar Saboda Kisa –Matasan Arewa A Kudu

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Arewa da ke Kudancin Nijeriya ta yi kira da babbar murya ga ‘yan kasuwa masu safarar kayan abinci zuwa yankin Inyamurai da ke kudu maso gabashin kasar nan su dakatar zuwa wani lokaci saboda abin da ta kira “hallaka masu safarar” da ake yi a yankin.

Matasan sun yi kiran ne a wani bayani da suka aike wa LEADERSHIP Hausa ta hannun shugabansu, Alhaji Ibrahim Ya’u Galadanci.

A ta bakin gamayyar, wannan cin fuska da tsangwama da kyama da neman haddasa fitina da tsagerun Inyamurai ke wa ‘yan arewa sun dade suna faruwa kuma babu wani kwakkwaran mataki da gwamnati ta dauka domin ganin an yi wa guru hanci.

“Lallai muna kira ga kungiyoyinmu na arewa masu kai abinci da dabbobi yankin Inyamurai su guji kaiwa. Abubuwan da ake wa ‘ya arewa a yankinsu ya kazanta. Ta yaya mutumin da yake kai maka tallar kayan abinci har gidanka amma zai zama abokin gabanka, babu wanda za ka wulakanta sai shi, abin ma har ya zama ana kashe su.

Wannan abin ya sha faruwa ba sau daya ba, ba sau biyu ba, ya faru sau da dama amma me aka yi? Don haka mutanenmu su dakatar da shiga yankin Inyamurai da sunan kai kayan abinci da dabbobi tun da duk cinikin da mutum yake ganin zai samu a can sai in yana da rai ne zai mora ko, idan kuma mutum ya kai kaya aka kona kayan, shi kuma aka kashe shi, ka ga an yi biyu babu.”
Alhaji Ibrahim ya ce ko a kwanan baya an ga yadda wasu tsagerun Inyamuran suka cinna wa wata motar shanu wuta, suka jikkata masu kayan.

Ya kara da cewa, “Domin yadda ake hallaka direbobin tirelolin da ke kawo kaya daga arewa ya kamata a guje su, saboda gwamnati ta yi shiru ta zuba musu ido ko kuma mene ne gwamnatin take nufi da hakan.” In ji shi.

Dangane da abin da ya faru na batancin addini a Sakkwato kuwa, Alhaji Ibrahim ya bai wa gwamnati shawarar kafa wata doka da za ta yanke hukuncin kisa ga masu batancin addini.

“Maganar cin zarafin Manzon Allah (SAW) da wata ta yi, dole ne gwamnati ta yi dokar hukuncin kisa idan tana son zaman lafiya a kasarmu, domin wallahi, wallahi, wallahi jinin jikinmu mun ba wa Manzanmu Annabi Muhammadu (SAW).” In ji shi.

Har ila yau, gamayyar kungiyoyin matasan ta yi kira ga musamman matasa su yi wa kansu kiyamullaili su guji sharrin ‘yan siyasa da za su nuna musu so a fili amma a boye makiyansu ne.

“Matasa ku yi kokari ku kiyaye kanku da sharrin ‘yan siyasar kasar nan da ba sa kaunarku, babu abin da za su yi muku illa su kai ku su baro.

A karshe muna masu yi wa kasarmu addu’ar zaman lafiya mai dorewa. Wadanda suke kokarin tayar mana da hankali mun yi tawassali da sunayen Allah tsarkaka ya yi mana maganinsu sabo da martabar Annabi Muhammadu (SAW).” Ya bayyana.

Related Articles

One Comment

  1. Wannan gaskiya ne cutarwa tayi yawa da ace wannan kungiya zatayi yajin aiki na wasu kwanaki ko watanni da yan kudu sun shiga taitayinsu zasugane yan arewa suna da amfani sosai a yankinsu, Amma sai dai kash idan kunfara ma sai aga ko sati bakwayi kuke janyewa sakamakon rashin hadinkanku, saboda ni ganau ne ba jiyauba Dan yanzu haka Ina kudun Ina ganin yadda sukeyiwa hausawa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button