News

Da Dumi-dumi Kotu Ta Yankewa Mubarak Bala Hukuncin Shekara 24 A Gidan Yari Kan Aikata Batanci

Kotu ta daure Mubarak Bala shekara 24 a gidan yari kan aikata saɓo

Kotu ta ɗaure Mubarak Bala shekara 24 a gidan yari kan laifin ɓatanci ga addinin Islama.

An yanke masa hukunci ne kan laifuka 18 da aka zarge shi ciki har da amsa laifin aikata sabo a gaban kotu.

Sai dai ya shaida wa kotun cewa lokacin da ya yi rubutu bai san cewar saƙon zai iya haifar da tashin hankali ba, sannan kuma hakan ya zama darasi a gare shi, nan gaba.

An kama Mubarak Bala, shugaban kungiyar wanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya, a ranar 28 ga watan 2020 a gidansa da ke jihar Kaduna, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano bisa zargin aikata sabo ta hanyar wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook

Sakon da ya wallafa ya fusata al’ummar musulmi a Najeriya.

Wata babbar kotu a Kano da ke arewacin Najeriya ta sake aike wa da Mubakar Bala zuwa gidan gyaran hali, saboda ci gaba da tsare rayuwarsa da kuma gazawar lauyoyinsa na gabatar wa kotun da cikakaken takardun da za su tabbatar mata cewar yana fama da rashin lafiya.

An karanto wa Mubarak Bala caji 14 da ake tuhumarsa a kai na yin sabo.

Yayin zaman kotun, an karanto masa sakonnin da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Facebook, wadanda ya yi kalaman batanci ga addinin Musulunci.

Ya amsa dukkan caji 14 da aka karanto masa da cewar ya aikata dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Ganin haka sai lauyansa ya roki kotun ta ba shi damar ganawa da wanda yake wakiltar, wato Mubarak Bala, kuma bayan ta amince, ya yi kokarin nuna ma sa tasirin cewa ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa.

Amma bayan da lauyan ya sanar da kotun cewa Mubarak Bala na son sauya amsar da ya bayar a gaban kotun, sai alkalin ya sake tambayar wanda ake tuhumar ko haka lamarin yake.

Mubarak Bala ya sanar da kotun cewa ba zai sauya amsa laifinsa da ya yi a gaban kotun ba.

Alkali kotun ya tambaye shi ko ya fahimci nauyin abubuwan da yake cewa, kuma wanda ake tuhumar ya amsa cewa ya fahimci komai.

Ya kara da cewa babu wanda ya tursasa masa don ya amsa dukkan laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa. Sannan ya ce babu wanda yayi masa wani alkawari, ko ya sanya masa wani ra’ayi, sai dai ya bukaci kotun ta yi masa sassauci da kuma adalci.

Wakilin BBC da ke kotun ya ce kotun na ci gaba da sauraron shari’ar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button