Religion

Naji Dadi Da Aka Dakatar Da Sheikh Nuru Khalid Daga Limanci — Inji Datti Assalafy

Naji Dadi Da Aka Dakatar Da Sheikh Nuru Khalid -inji Datti Assalafy

Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ‘yan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja ya dakatar da wani gorbataccen Malami karnen farautar Yehhudu jagoran masu yada akidar daidaita tsakanin addinai (INTER-FAITH) a Nigeria daga Limanci a Masllacin

Malamin wanda yayi fice wajen jefa soyayyar al-kuffaru a cikin zukatar Musulmai an dakatar dashi ne saboda yayi khuduba ranar juma’a ya caccaki Gwamnatin Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya cewa idan ba’a samar da tsaro ba to wai Musulmai suki fita zabe

Shi dai Shehi Al-interfaith ba Sarkin Musulmi bane, ba Musulmai yake wakilta gaba daya ba, kuma bai da ikon ya hanamu fita zabe, sannan ba duka kowani yanki na Nigeria bane yake fama da matsalar tsaro, duk bala’in ta’addanci da aka yi a Gwamnatin Jonathan bai hana a fito zabe ba

Allah ne Ya kama jagoran masu yada addeenin Interfaith, yana fakewa da sukar Gwamnatin Buhari yana yada akidar daidaita tsakaaninn addeenai, ba shakka Allah ba zai barshi ba, barnann da wannan malami yake yiwa Musulunci ya wuce barnonin da aka yiwa Musulunci a Gwamnatin Buhari, domin shi ruhi da imani yake rugujewa ba gangar jiki ba

Idan zai kwana ya tashi yana sukar Gwamnatin Buhari ba ruwana dashi, amma da kunsan illar da wannan Shehi Al-interfaith yake yiwa Musulunci akan manufar Yehudawa (Intafait) da baku tsaya bata lokacin ku a kansa ba, shiyasa masu karin magana sukace rashin sani yafi fare duhu

Alhamdulillah Interfaith taci bayaa a Nigeria, hanyoyin kamun Allah suna da yawa
Allah Ka dada mayar da su baya

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button