News

Da Dumi-dumi: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana Yau Da Aminu Adam Wanda Ya Zagi Aisha A Villa.

Da Dumi-dumi: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana Yau Da Aminu Adam Wanda Ya Zagi Aisha A Villa.

Bayan Uwargidar Shugaban Kasa Ta Yafe Masa, Aminu Zai Gana Da Buhari A Villa Yau.

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu Na Cewa, Matashin Nan Da Ake Zargi Da Yin Rubutun Batanci Ga Matar Shugaban Kasa Zai Gana Da Buhari.

Matashin dan asalin jihar Jigawan wanda ya zagi Hajiya Aisha Buhari, uwargidar shugaban kasa, Aminu Mohammed Adamu, ya samu yanci yanzu haka.

Aminu wanda tuni an sakeshi daga kurkukun Suleja zai kuma gana da mijin Aisha, wato Shugaba buhari kafin ya koma wajen iyayensa, kamar yadda rahoton Leadership ya naqalto.

Wanda ke matsayin Uba ga Aminu, Malam Kabiru Shehu, ya bayyana hakan, Shehu ya ce Aminu yanzu haka yana Aso Villa kuma yana shirin ganawa da Shugaba Buhari.

Aminu Dai An Kama Shi Da Zargin Cin Mutumci Wa Matar Shugan Kasa, Lamarin Da Yasa Aka Gabatar Dashi A Gaban Alkali.

Wanda Alkali Ya Aike Dashi Gidan Gyaran Hali

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button