News

Yanzu-Yanzu Aisha Buhari ta janye karar da ta kai Aminu Muhammad, kamar Yadda lawyansa C.K. Agu ya shaida wa bbc

Yanzu-Yanzu Aisha Buhari ta janye karar da ta kai Aminu Muhammad, kamar Yadda lawyansa C.K. Agu ya shaida wa bbc

Rahotannin Da Muke Samu Yanzu-yanzu Na Cewa, Uwar Gidan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Aisha Buhari.

Ta Janye Karar Da Ta Shigar Da Wani Matashi Mai Suna Aminu Adamu Bisa Zarginsa Da Yin Kalaman Batanci Akanta A Shafin Tiktok.

Tun Bayan Shigar Da Karar Ne A Gaban Kotu Alkali Ya Aike Da Matashin Gidan Gyarin Hali Lamarin Da Ya Fusata Yan Nigeria Inda Sukaita Korafi Akai.

Lamarin Da Yasa Ƙungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta ce ya zama wajibi ga hukumomin Najeriya su saki matashin nan da ake zargi da cin mutuncin uwargidar shugaban ƙasar Muhammadu Buhari tare da yin watsi da duk zarge-zargen da ake yi masa.

A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce ta samu rahotannin da ke cewa an azabtar da matashin bayan kama shi.

Ta ce “babban abin kunya ne a ce hukumomin Najeriya sun kama tare da azabtar da Aminu Adamu kawai saboda ya wallafa bayanai a shafin tuwita wanda ya shafi uwargidar shugaban ƙasar.”

Bayanin ya ƙara da cewa wannan lamari karan-tsaye ne ga ƴancin bil’adama.

Haka nan hukumar ta ce abin da ya kamata hukumomin ƙasar su mayar da hankali a kai shi ne tsarewar da aka yi wa matashin ba bisa ƙa’ida ba da kuma azabtar da shi da aka yi.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa kotu ta tura matashin mai suna Aminu gidan gyara hali, bayan da aka gurfanar da shi bisa zargin sa da cin mutuncin mai-ɗakin shugaban ƙasa, A’isha Buhari a shafinsa na tuwita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button