![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/05/FB_IMG_1652703134473.jpg?resize=720%2C405&ssl=1)
DA DUMI-DUMINSA: Gwamnatin Jihar Borno Ta Hana Musulman Jihar Gudanar Da Zanga-zangar Nuna Bacin Ransu Kan Munanan Kalaman Batanci Da Wata Budurwa Ta Yi Akan Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad SAW A Jihar.
![](https://i0.wp.com/www.arewanewseye.com/wp-content/uploads/2022/05/FB_IMG_1652702680642.jpg?resize=211%2C300&ssl=1)
A safiyar yau Litinin daruruwan mutane sun yi dafifi kan titin Division 7 dake Maiduguri domin yin zanga-zangar nuna bakin ciki kan kala*man ba*tanci ga Annabi Muhammad SAW da wata mai suna “Noami Goni” ta wallafa a shafin sada zumunta na Facebook wanda ya haifar da ri*kici a yankin.
Gwamnatin jihar ta tura jami’an rundunar da suka hada da sojojin Najeriya, ‘yan sandan Mobile, jami’ai masu yaƙi da ta’addanci ‘Counter-Terrorism Unit’ (CTU), Anti-Bomb Squad (EOD), “Crack Team” NSCDC, a yankin domin kwantar da tarzoma da halin da ake ciki.
Har zuwa yanzu da muke kawo muku wannan rahoton, ba a ka*ma budurwar ba.
Me za ku ce?