News

Dan Jarida Jaafar Jaafar Yayi Martani Ga Masu Tausayawa Makashin Haneefa Inda Ya Bukaci Akarya Mai Kafa In Za’a Kawo Shi Kotu

Social Media Tayi Chaa Kan Masu Tausayawa Makashin Haneefa Wato Abdulmalik Mohammed Tanko.

A Jiya Ne Aka Tashi Da Ganin Baiyanar Wani Bidiyo, Wanda Aka Wallafa A Shafin Jaridar Muryar Amurka VOA.

Cikin Bidiyon Anga Yadda Jama’a Da Dama Suka Tausayawa Makashin Haneefa Abubakar Duba Da Kalaman Da Yai A Cikin Guntun Bidiyon Zakuma Ku Iya Kallon Bidiyon A Kasan Rubutun Nan.

Jama’a Da Dama Ne Suka Tausayawa Makashin, Tare da Wallafa Hakan A Shafukan Sada Zumunta Da Cewar Haka Kaddarar Sa Take Kuma Kowa Baifi Karfin Kaddara Ba.

Lamarin Dai Ya Dauki Hankali Tare Da Janyo Cece Kuce A Shafukan Na Sada Zumunta Inda Mutane Suka Shiga Baiyana Ra’ayoyin Su Akai.

Ciki Kuwa Harda Fitaccen Dan Jaridar Nan Jaafar Jaafar Wanda Ya Wallafa A Shafin sa Na Sada Zumunta Cewa.

“Shegen da ya kashe yarinyar bai san ya tausayawa iyayenta ya hakura da kudin fansa ba, shi ne wai wasu ke tausayawa?

Rashin imanin da wannan tsinanne ya nuna wajen raba yarinya da iyayenta da bata guba da cusa gawarta cikin buhu da binne ta cikin datti da bibiyar neman kudin fansa, ya nuna cewa mutumin nan ba yau ya fara ba. Idan aka matsi shege da kyau, za’a gano laifuffukan da ya yi a baya.

Idan ‘yansanda za su karya barawon akuya, to ya kamata su kawo mana wannan shege kotu yana dingishi kuma sun zubar masa hakoran gaba.

Gadai Bidiyon Da Yasa Jama’a Tausayawa Makashin Nan Ku Kalla

https://youtu.be/fnnAlHacreI

Related Articles

One Comment

  1. Wannan mutum bashi da woni imani don Allah mutane su deina yewdaran kansu wai suna tausaya Masa, ta Yaya zaka tausaya wa mara imani,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button