News

DASHEN ƙODA: Mawaki Eedris Abdulkareem Na Neman Taimakon Addu’a Tare Da Taimakon Tallafin Kudi Daga Yan Nigeria

DASHEN ƙODA: Mawaki Eedris Abdulkareem Na Neman Taimakon Addu’a Tare Da Taimakon Tallafin Kudi Daga Yan Nigeria

Dashen ƙoda: Mawaƙi Eedris Abdulkareem ya fitar da asusun tallafi ‘GoFundMe’

Shahararren mawakin nan na Najeriya, Eedris Abdulkareem, ya raba asusun sa da ya yiwa laƙabi da GoFundMe ga masoya da kuma ƴan ƙasa domin a tallafa masa bisa aikin dashen ƙoda da za a yi masa.

A kwanan nan ne dai shahararren mawakin wakokin zamanin ya kamu da cutar koda har ta kai ga an kwantar dashi a asibiti.

Abdulkareem, wanda ya wallafa a shafinsa na Instagram, inda ya bada cikakkun bayanai na asusun sa na GoFundMe da aka kirkira don taimakon kudin magani, ya ce yana jiran likitoci ne kawai su kira shi domin a yi masa aikin.

Ya ce masoya ne su ka nemi da ya buɗe asusun na GoFundMe.

Ya godewa masoyansa da masu yi masa fatan alheri bisa nuna kauna da goyon bayan da suka nuna, tun bayan sanar da labarin lafiyar ta sa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button