Kannywood News

GASAR ‘ƘIDAYA CHALLANGE: Bidiyon Yadda Abis Fulani Da ‘Yan Arewa Suka Watsa Wa Mawaƙi Rarara Kasa A Ido

GASAR ‘ƘIDAYA CHALLANGE: Bidiyon Yadda Abis Fulani Da ‘Yan Arewa Suka Watsa Wa Mawaƙi Rarara Kasa A Ido

DAGA EL-ZAHARADDEEN UMAR

Yanzu haka dai alamu na nuni da cewa gasar rawa ko rawa da fitaccen mawaƙin siyasar nan Dauda Adamu Abdullahi (Rarara) ya saba sanyawa musamman ga mutane masu ta’amuli da soshiyal midiya ta samu cikas.

A wannan karon, kamar yadda ya saba, Rarara ya sanya gasa ne a kan sabuwar waƙar sa da ya yi ta yin kira ga al’umma a kan batun ƙidaya da Gwamnatin Tarayya ta shirya, manufa dai ya na son wannan saƙo ya shiga lungu da saƙo na Nijeriya, musamman na Arewa.

Mawaƙin ya na ware wasu kyaututtuka da ake raba wa waɗanda su ka yi zarra a gasar, kamar yadda ya yi a gasar waƙar ‘Baba Buhari Ɗoɗar’ da waƙar Sha’aban Sharaɗa.

A cikin wannan makon da mu ke ciki babu batun da ya dabaibaye soshiyal midiya kamar wannan batu da ya kira da ‘Kidaya Challenge’. Yayin da wasu na suka, wasu kuwa na yabo, amma dai masu sukar sun fi yawa, wanda hakan ya sa wakilin mujallar Fim ya bibiyi lamarin.

Babbar ta hannun damar mawaƙin, A’isha Ahmad Idris (Ayshatulhumairah), ita ce ta fara bada sanarwar gasar a TikTok inda ta yi dogon bayani kan shirye-shirye da tsare-tsaren yadda gasar za ta kasance da irin kyaututtukan da za a raba wa waɗanda su ka yi nasara.

Yin sanarwar ke da wuya jama’a su ka fara maida martani marar daɗi inda wasu ke cewa su yanzu ba wannan ba ce a gaban jama’ar Arewa, matsalar tsaro ita ce abin da ya fi damun su.

A wannan ɓangare kuwa, wasu na sukar gasar ne da cewa Rarara ya karɓo kwangila mai ƙarfin gaske, ya zo ya gutsura wa mutane ɗan abin da bai taka ƙara ya karya ba, don ya lura da halin ƙuncin da al’umma ke ciki.

Wasu har da yin barazana ga duk wani mai amfani da TikTok da cewa duk wanda ya yi wannan gasar kuma ya ɗora a shafin sa to a ƙaurace masa, a daina bibiyar sa baƙi ɗaya.

Ta wani ɓangaren kuma akwai masu ra’ayin komai zai faru ya daɗe bai faru ba, sai sun yi gasar tunda kuɗi za su samu, kuma su na da buƙatar kuɗi.

Su kuwa mutanen Rarara, bayan sun lura da cewa jama’a da dama sun juya wa wannan lamari baya kuma sun fara fusata da mawaƙin, musamman su na sukar sa da cewa ana famar kashe-kashe a Arewa amma ba a ji ya yi waƙar kira ga gwamnati da ta ɗauki mataki ba sai kawai aka ji ya na sanya gasa kamar yadda ya saba.

Ba su yi wata-wata ba wajen maida martani da faɗin cewa su dai kam, sai dai a kar tsohuwa akan daddawar ta, har ma su na kawo wata waƙa da mawaƙin da sauran mawaƙa na ƙungiyar 13×13 su ka yi a kan batun matsalar tsaro, tare da faɗin cewa ina jama’a su ke lokacin da mawaƙin ya yi wannan waƙar?

Kazalika ita ma A’ishatulhumaira da ta bada sanarwar, bayan ta lura da cewa kashi mai yawa na jama’ar da su ke sa ran cewa za su yi wannan gasa sun juya mata baya, sai ta sake fitowa a TikTok ta ƙara yin dogon bayani.

A bidiyon da ta ɗora, mai ɗauke da hoton Rarara da na Shugaban Hukumar Kidaya ta Ƙasa (NPC), Alhaji Nasir Isa Kwarra, jarumar ta Kannywood ta bayyana cewa wannan gasa babu dole, ba a ce sai mutum ya yi ba.

Ta ƙara da cewa wannan aiki na ƙidaya fa zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a arewacin Nijeriya.

Haƙika wannan kalami bai yi wa jama’a daɗi ba, baya ga maida martani wasu sun bi ta da ashariya a yayin da wasu kuma nasiha su ka yi mata.

Yanzu dai a iya cewa wannan gasa ta haɗu da tasgaro; duk da halin ƙuncin da al’umma ke ciki kuma su na buƙatar kuɗi amma su ka kau da kan su daga wannan gasa tare da faɗin su matsalar tsaro ta dame su ba gasa ba.

Shin ko yaya Rarara ya ji da kuma lura da wannan ce-ce-ku-ce da ake yi a kan wannan gasa?

Mujallar Fim ta tuntuɓe shi ta wayar tarho domin jin nasa ba’asi kan wannan tirka-tirka, sai dai kash! wayar sa a kashe ta ke.

Shi ma mai taimaka wa mawaƙin ta fuskar yaɗa labarai, Rabi’u Garba Gaya, bai dauki wayar da wakilin mu ya yi masa ba ko ya amsa saƙon tes da ya tura masa domin jin daga ɓangaren su har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button