News

Gaskiyar Lamari Dangane Da Abinda Ya Faru Game Da Rasuwar Sheikh Bagoni Asami Gashua

Gaskiyar Lamari Dangane Da Abinda Ya Faru Game Da Rasuwar Sheikh Bagoni Asami Gashua

Mallam ya kamo hanya daga Kano zuwa Gashua. Yana zuwa bakin Barikin Soja na Nguru, sai yaga wani Soja me alamar yana jiran motar da zata daukeshi ne.

Kazalika kuwa sai ya nemi alfarmar a rage musa hanya zuwa Jaji-Maji. Sojan yana dauke da irin gadon nan na tafida-gidanka (Camp Bed). Sojan yana cikin farinkaya ne ba inifam ba.


Ashe akwai bindiga AK-47 cikin wannan Camp Bed shi Mallam bai ankara ba.

Suna zuwa wani gari me suna Chakama sai Mallam yace zai sauka ya kama ruwa. Sai wannan Soja me dauke da gado yayi amfani da wannan dama ya ciro bindigar yayi masa harbi har Ukku nantake ya kashe shi.
Bayan ya kashe shi, sai ya nemi wani abokin sa dake wajen da ya taimaka masa don su gudu da motar, amma sai motar taki tashi.

To su kuma mutanen wannan kauye da suka ji kara sun zata ma hatsari akayi, sai suka garzaya don su bada taimako sai suka fahimci asalin abinda ya faru. Nantake suka sanarda Jami’an tsaro suka kama wadannan sojojin kuma yanzu haka suna nan Damaturu ana cigaba da Bincike akansu.

Da bakinsa sojan da yayi kisan ya bayyana haka.

Sunan sojan da yayi kisan Lance Corporal JOHN GABRIEL, shi kuma wanda yayi niyyar taimaka masa ADAMU GIDEON dake karkashin Bataliyar Soja ta 241dake Garin Nguru.
Da aka tambayi sojan dalilin yin hakan sai yace yayi hakan ne don ya gudu da motar Mallam din yaje ya sayar.

Duk wani zance ba wannan ba, jitajita ne kawai wanda bashida tushe balle makama.

Allah SWT ya saka wa Mallam wannan abinda akayi masa, ya saka mana tareda iyalansa makusanta da sauran Musulmi.
Allah ya kyautata karshenmu bakidaya, Allahumma Ameen.”

Auwal El-Yobawi Bayamari

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button