News

Gwamnatin tarayya ta fitar da sabon Albishir na baiwa “Yan Najeriya Miliyan 37 tallafi

Gwamnatin tarayya ta fitar da sabon Albishir na baiwa “Yan Najeriya Miliyan 37 tallafi

Gwamnatin tarayya ta sanar da fara baiwa matasa da basu yi karatun Boko ba da kuma Marayu da masu nakasa tallafi.

Gwamnatin tace zata bayar da tallafinne a karkashin tsarin GEEP kuma mutane Miliyan 37 zasu amfana dashi.

Ministar Kula da Ibtila’i da Jinkai, Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana haka a wajan kaddamar da kwamitin da zasu kula da tsarin a Abuja.

Za’a tallafawa matasan su samu bashin da babu ruwa a karkashin tsarin ta yanda zasu kula da kawunansu da samawa kansu sana’o’i masu kyau.

Ministar ta bayyana cewa, an samar da wakilai 774 a kowace karamar hukuma dake Najeriya da kuma cikin Abuja dan su jagoranci matasan kan yanda zasu amfana da wannan tsari.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button