News

Harin Jirgin ƙasa: Har Yanzu Ina Matuƙar Son Baba Buhari, In Ji Fasinjan Da Ya Kuɓuta Daga Hannun ƴan Ta’adda

Harin Jirgin ƙasa: Har Yanzu Ina Matuƙar Son Baba Buhari, In Ji Fasinjan Da Ya Kuɓuta Daga Hannun ƴan Ta’adda

Hassan Usman, lauya kuma ɗaya daga cikin waɗanda harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya rutsa da su, ya ce har yanzu masoyin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne.

A ranar 28 ga watan Maris, wasu ‘yan bindiga su ka kai hari kan wani jirgin ƙasa da ke kan hanyar Kaduna, inda aka kashe mutane da dama, aka kuma yi awon gaba da wasu.

Hassan na daga cikin fasinjoji hudu da aka sako daga hannun masu garkuwar a ranar 25 ga watan Yuli.

Da yake magana a wata hira da ICIR, ya ce duk da cewa gwamnati mai ci ta gaza a fannin tsaro, amma har yanzu “ni ina matuƙar son Buhari .”

“Har yanzu ni masoyin Buhari ne , amma ta fuskar tsaro zan iya baiwa wannan gwamnati maki kaɗan, domin ɗaya daga cikin babban nauyin da ke wuyansu shi ne ganin gwamnati ta tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ƴan kasa,” inji shi. .

“Amma kamar yadda yake a yanzu, zan iya cewa gwamnati ta gaza sosai a fannin tsaro. Duk da ɗumbin kuɗaɗe da aka ware domin tsaro a Nijeriya, babu wani abu da ake gani a ƙasa”

Ya ƙara da cewa abin da ya fuskanta a lokacin da yake tsare yana da matuƙar muni.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button