NewsReligion

Hisbah Ta Kama Matasan Da Basa Azumi A Kano Mata Da Da Maza

Hukumar hisbah ta jihar kano ta sanar da kama wasu matasa su goma sha daya 11 suna cin abinci da tsakar rana.

Matasan dai sun hada da maza su takwas 8 dakuma mata su uku 3.

Hkumar ta hisbah ta kara da cewa zata gudanar da bincike ga matasan dan gano dalilin da yasa basu dauki azumin ba.

Ba wannan ne karo na farko da hukumar ke gudanar da kame irin wannan ba a jahar kano.

Hukumar na yin irin wanna kame a kowacce shekara cikin watan azumin ramadan.

Azumi dai farilla ne ga kowanne musulmi kuma balagagge wato baligii.

Sai dai in da lalura ko kuma haila ga mata ko kuma tsofaffi wadanda basa iya rike yunwa.

Anan mukeso daku bayyana mana ra’ayoyinku shin mai kuke ganin yana hana matasa yin azumi acikin watan ramadan?

Kuma a ganin ku wanne irin mataki yakamata hukumomi su dauka akan matasa kuma balagaggu wadanda aka kama basa azumi?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button