NewsPolitics

Yadda Ganduje Yai Sasanci Tsakanin Dangote Da Abdussamadu BUA Manyan Yan Kasuwar Africa Kuma Yan Asalin Jahar Kano

Gwamnan jahar kano Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci zaman sasanci tsaakanin hamshaqan masu kudin jahar kano Alhaji Aliko Dangote Da Alhaji Abdussamadu Isyaka Rabi’u BUA.

A wata wallafa da gwamnan yai a shafinsa na facebook an rubuta cewa andai yi zaman sulhun ne tsakanin hamshaqan yan kasuwar biyu dakuma wasu masu fada aji a jahar dakuma jami’an gwamnatin jahar.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa ricikin hamshaqan yan kasuwar ya samo asali ne akan batun farashin suga a kasuwannin nigeria.

Kamar yadda shafin jaridar Premium times ya rawaito cewa tun dafarko dangote ne ya zargi BUA da yin amfani da wata dama ta hanyar da bata dacee ba. Yayinda anashi bangaren shima Abdussamadu Mai Kamfanin BUA yace Dangote naso ya mamaye kasunni tare da saka farashin da yaga dama.

Amma a wata sanarwa da tagabata Alhaji Aliko Dangoten yayi fatali da zargin sanya farashin da yaga dama.

Wannan musayar yawun da akai tatayi ne tsakanin manyan yan kasuwar africa kuma yan asalin jahar kano yasa gwamnan ya gayyace su domin sasanci a tsakani saboda irin gudun mawar da suka baiwa jahar kanon dama kasa baki daya.

Sai dai yan kasuwar sun karyata jita jitar dake yawo cewa wai dangote ne ya gayyaci abdussamad domin kara kudin sugari inda suka tabbatar da cewa zancen baida tushe balle makama.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button