News

Amfani da Dan Tsami a Kano Mutum 10 Sun Mutu Mutum 400 Na Kwance A Asibiti

Rahotanni na cewa Akalla Mutane kusa guda goma ne suka rigamu gidan gaskiya yayinda akalla mutum dari hudu ke cigaba da amsar magani a asibiti sakamakon Yin amfani da lemon dake dauke da sinadarin dan tsami

Kwamishinan lafiya na jahar kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan acikin wani bidiyom da aka rabawa manema labarai yau Alhamis a jahar kano.

Kwamishinan Yakara Da Cewa.. Cikin wadanda suke karbar maganin a asibiti akwai wasu guda hamsin 50 da suka kamu da ciwon hanta.

Haka zalila kwamishinan ya shawarci jama’a da suguji yin Amfani da dan tsami musamman ma acikin waannan wata na azumin ramadan domin kaucewa yin amfani da wanda ya riga da ya lalace.

Anan muke addu’ar ubangiji Allah Ya Kare mu Ya Tsare ya kare Al’ummar musulmi daga Fada Cikin Wannan Iftila’i

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button