Rahotanni Daga Jamhuriyar Niger Na Cewa An Gudanar Da Jana’izar Yara Yan Makarantar Boko Su 20 Wadanda Iftila’in Gobara Yai Sanadiyar Rasa Rayukan Su

A ranar 14 ga watan nan da muke ciki ne gobarar ta tashi a wata makarantar boko dake anguwar pays bass a babban birnin yamai.

Haka zalika rahoton ya kara da cewa kimanin ajujuwa 25 acikin 35 iftila’in gobarar ya shafa wanda kuma yai sanadiyar rasa rayukan yara kananu masu shekaru 5 zuwa 10.

Kazalika wannan iftila’in gobara ya daga hankulan mutane da dama musamman ma a jamhuriyar ta niger dakuma kasar nigeria

Anan muke addu’ar ubangiji Allah Ya Jikansu Yakuma bawa iyayensu hakurin jure wannan rashi ubangiji ya kiyaye gaba Amin.

Click Here To Drop Your Comment