News

Hukumar NDLEA ta sakeyin Babban kamu Na Wasu Jabun dalolin Amurika miliyan 4.7 a Abuja

Hukumar NDLEA ta sakeyin Babban kamu Na Wasu Jabun dalolin Amurika miliyan 4.7 a Abuja

Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA sun dakile wani yunkurin wata kungiya na tura dala miliyan 4.7 na bogi a cikin tattalin arzikin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan kama wani kayyaki ne a unguwar Abaji da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar 18 ga watan Fabrairun 2022 da aka aika daga Legas zuwa Abuja.

Duk da haka, an kama wani mutum mai shekaru 42 da ake zargi da hannu a cikin wadanda aka kama tare da kudi da kuma wadanda ake zargi da ke tsare a mika su ga Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, don ci gaba da bincike.

A halin da ake ciki, hukumar ta kuma kama wasu mutane 3 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da fiye da kilogiram 300 na haramtattun kwayoyi da suka hada da canabis sativa, tramadol, diezapam da kuma allurar allurar pentazocine da dai sauransu, a kwara da Adamawa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button