News

Innalillahi An Kuma Sace Gwamman Manoma A Jihar Niger

Wasu daga cikin mazaunan ƙauyen na Kaffin-Koro sun shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigan sun shafe tsawon sa’o’i suna cin karensu babu babbaka, lamarin da ya tilasta wa mutane da dama tserewa.

Rahotanni daga jihar Neja a Najeriya na cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da manoma a wani ƙauye da ke karamar hukumar Paikoro.

An kai hari ne a ranar Labara a yankuna da dama da ke ƙauyen, sannan akwai mutum ɗaya da aka kashe.

Babu dai wasu cikakkun bayanai kan adadin manoman da aka yi garkuwa da su, sai dai yankin Neja na daga cikin yankunan Najeriya da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga domin neman kudin fansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button