News

Innalillahi: Yan Mata 15 Sun Nutse A Ruwa A Jihar Sokoto

Akalla ƴan mata 15 ne suka rasu bayan kifewar kwale-kwale a ƙauyen Dandeji da ke karamar hukumar Shagari na jihar Sokoto.

An ruwaito cewa ƴan matan na kan hanyarsu ta zuwa wani daji da ke kusa domin neman itace lokacin da kwale-kwalen da suke ciki ya kife a safiyar yau Talata.

Wakilin mu ya rawaito cewa, cewa ƴan mata sama da 40 ne ke cikin kwale-kwalen lokacin da lamarin ya faru, a cewar shaidu.

Wani mazaunin yankin mai suna Muhammad Ibrahim, ya ce an gano gawawwaki 15 kawo yanzu, inda ya ce masu ninƙaya na ci gaba da neman sauran waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Shugaban karamar hukumar ta Shagari, Aliyu Abubakar, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ana shirin yi wa mutanen jana’iza.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button