News

Tirqashi: Wazirin Zazzau Ya Bukaci A Tsige Sarkin Zazzau

Zaman kotun na yau Talata dai ya maida hankali ne akan hujjojin da layoyin wadanda ake kara ke dogaro da su na bukatar kotu ta yi watsi da karar da kuma hujjojin layoyin masu kara na cewa kotu na da hurumin sauraron karar.

Babban kotun jahar Kaduna da ke sauraron karar da Wazirin Zazzau da aka cire, Ibrahim Mohammed Aminu ya shigar ya na bukatar a cire Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, kan cewa nadin ya sabawa ka’idojin nadin sarki, ta ce za ta sanar da ranar yanke hukunci nan ba da dadewa ba.

Bayan fita daga zauren kotun ne lauyan da ke kare mai martaba Sarkin Zazzau da masarautar, Abdul Ibrahim wanda babban lauya ne na Kasa wato SAN, ya ce lallai kotun ba ta da hurumin sauraron wannan kara.

Daga bisani alkalin kotun mai shari’a Isah Aliyu ya dage zaman kotun zuwa wata rana da zai sanar nan gaba domin yanke hukunci akan hurumin kotun da cancantar Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu a matsayin mai-kara.

A cewar Lauya Ibrahim, mai karar ma bai da wani hurumin kai karar domin baya cikin ahalin gidan sarautar, saboda haka katsalandan ne ma ya sa shi shigar da karar.

Shi dai Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Mohammed Aminu wanda aka cire daga mukamin Wazirin a baya, ya na karar gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i da mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli da kuma wasu mutane 12, bisa taka doka da ka’idojin nadin sarki a masarautar Zazzau.

Sai dai layoyin mai kara da su ka tattake guri a cikin kotun bisa hujjojin da su ka ce su na dasu kan hurumin kotun, sun ce ba da ka su ke magana ba don su na da madogara a dokokin Najeriya.

Lauya Bashir M. Bello na cikin layoyin mai kara, kuma ya ce ba su da haufi akan hujjojin da su ka gabatar.

Lauya Bello ya ce duk sassan doka da ke nuna halaccin kotun jihar Kaduna ta saurari wannan kara su na cikin hujjojin da su ka gabatarwa kotun.

Akan haka yake bukatar a cire Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli saboda baya cikin jerin sunayen da masu zaben sarki su ka gabatarwa gwamnan jahar Kaduna a lokachin zaben Sabon Sarki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button