News

Innalillahi: Yanbindiga Sunkai Hari Jami’ar Plateau Plasu

‘Yan bindigar sun mamaye ɗakunan kwanan ɗalibai mata a makarantar da ke Bokkos a cikin dare, kamar yadda hukumomin makarantar suka bayyana, to sai dai sun ce ‘yan bindigar ba su kama ɗalibai ba.

Hukumomin jami’ar jihar Plateau (PLASU) da ke tsakiyar Najeriya sun ce jami’an tsaron makarantar sun daƙile wani harin ‘yan bindiga da suka kai makarantar ranar Talata da daddare.

”Da gaske ne ‘yan bindiga sun yi yunƙurin sace wasu daga cikin ɗalibanmu, to amma jami’an tsaron makarantar sun daƙile yunkurinsu”, in ji Mista Agams.

Jami’in hulɗa da jama’a na makarantar John Agams ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN faruwar lamarin.

Mista Agams ya ce ‘yan bindigar sun je jami’ar ne da nufin yin garkuwa da ɗalibai, to amma jami’an tsaron makarantar sun samu nasarar daƙile harin.

Ya ƙara da cewa ɗaliba ɗaya ta samu rauni sakamakon lamarin da ya faru.

Shugaban jami’ar Farfesa Benard Matur ya yi kira ga ɗaliban da su kwantar da hankali.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button