News

Innalillahi..; An Tsinci Gawar Wani Mutum Da Aka Yi Wa Kisan Gilla Bayan An Ƙwace Masa Mota A Jihar Katsina

Innalillahi..; An Tsinci Gawar Wani Mutum Da Aka Yi Wa Kisan Gilla Bayan An Ƙwace Masa Mota A Jihar Katsina

Wani Rahoto Da Muke Samu Yanzu-Yanzu Daga Comr Nura Siniya Na Cewa.

An tsinci Gawar wani mutun a cikin ƙwalbatin dake bakin filin wasa na Karakanda Stadium da ake zargin wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun kashe tare da ƙwace mashi mota a jihar Katsina.

Mutumin wanda yake matukin mota ne 406 kafin rasuwar tasa kamar yadda wasu shaidun gani da ido suka tabbatar.

Wasu shaidun gani da ido bayan an tsinci gawar sun bayyana cewa sun san mutumin wanda yana da motar ƙirar 406.

Inda tuni aka sanar da jami’an tsaro suka zo suka tafi da gawar domin ci gaba da gudanar da bincike.

Lamarin ya faru ne cikin dare inda aka wayi gari da ganin gawar tasa, a yau Talata da safe.

Allah Ya jiƙanshi da Rahama ya tona asirin miyagun mutanen da suka yi mashi wannan aika-aikar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button