Trending

Innalillahi.. Kalli Bidiyon Mutum shida Da suka mutu, 16 suka jikkata a hatsari mota a Bauchi

Innalillahi.. Kalli Bidiyon Mutum shida Da suka mutu, 16 suka jikkata a hatsari mota a Bauchi

Akalla mutum shida ne suka mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku ranar Lahadi a daidai ƙauyen Miya da ke ƙaramar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya.

Babban kwamandan hukumar kiyaye aukuwar hadura mai lura da shiyyar yankin Yusuf Abdullahi ne ya bayyana haka cikin wani rahoton aukuwar haɗura da ya aike wa kamfanin dillancin labaran ƙasar NAN ranar Lahadi a Bauchi.

Babban kwamandan na hukumar FRSC ya ce wasu ƙarin mutum 16 sun samu raunuka sakamakon hatsarin.

Lamarin ya rutsa da motar ɗaukar fasinja guda ɗaya ƙirar Toyota Hiace, da safiyar ranar Lahadi.

Ya kuma alaƙanta faruwar hatsarin da fashewar taya tare da kwacewar motar.

Ya ƙara da cewa “mutum shida sun rasa rayukansu manyan mata biyu da ƙananan yara huɗu”.

Yusuf Abdullahi ya ce an kai gawarwakin waɗanda suka mutu da sauran waɗanda suka jikkatan babban asibitin Kafin Madaki .

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button