Kannywood News

Shagalin Auren Lukman na shirin LABARINA da Amaryar sa Amina,Allah ya bada zaman lafiya

Shagalin Auren Lukman na shirin LABARINA da Amaryar sa Amina,Allah ya bada zaman lafiya

A yau Asabar ne 24 ga watan Disambar shekarar 2022 aka daura Auren jarumi Yusuf Saseen wanda mutane da dama sukafi sani da Lukman a cikin shirin Labarina mai dogon zango.

An daura auren ne dashi da Amina a garin Potistom dake jihar Yobe dake Najeiya.

Daurin Auren ya samu halartar manyan jarumai da dama harma da daraktoci da marubuta, cikin su sun hada da Aminu Saira,Isah Feruzkhan (Presdor),da dai kafatanin jarumai da marubuta shirin Labarina series.

Kafin daurin Auren anyi shagulgula da suka hada da Kwallon kafa,dinner din biki da dai sauran su kafin daga bisani har akaje Potistom din aka daura Auren a tsakanin Yusuf din da Sahibar sa Amina.

Daga karshe muna musu fatan Alkairi da Allah ya basu zaman lafiya.

Ba tare da bata lokaci ba zaku iya kallon cikakken bidiyon anan kasa, kuci gaba da kasancewa damu domin samun labarai da dumidumin su, mungode!

https://youtu.be/ADzexbimVS8

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button