News

Rashin Karfi Ne Ya Sa Muke Tura ‘Yarmu Talla Duk Da Cewa Aurenta Ya Karato, Cewar Iyayen Yarinyar Da Ta Ajiye Kayan Tallarta Tana Sallah A Bakin Hanya

Rashin Karfi Ne Ya Sa Muke Tura ‘Yarmu Talla Duk Da Cewa Aurenta Ya Karato, Cewar Iyayen Yarinyar Da Ta Ajiye Kayan Tallarta Tana Sallah A Bakin Hanya

ALHAMDULILLAH: An Sami Nasarar Gano Wacce Ta Kama Salla Lokacin Da Take Talla

Idan baku manta ba a kwanakin baya Jaridar Amintacciya ta rawaito muku cewa, wani mai anfani da kafafen Sada Zumunta Abdulmudallib Hamza Kibiya ne ya hangi wannan baiwar Allah tana Sallah dai dai lokacin da take yawon talla, ganin haka yasa ya dora a shafin sa na Facebook.

Sakamakon haka ne yasa labarin matashiyar ya zagaye kafafen Sada Zumunta inda jama’a da dama ke neman yadda za’a gano inda take.

Cikin ikon Allah kamar yadda ya bayyana, a yau ne ya sami haɗuwa da wannan baiwar Allahn wacce tai Sallah a kasuwa Bayan kwashe kwanaki 6 ana Nemanta.

Kamar yadda ya bayyana yanzu haka zai tafi da ita gidansu, domin suyi Magana da iyayenta.

Wane fata za kuyi mata ?

Daga Amintacciya

Rashin Karfi Ne Ya Sa Muke Tura ‘Yarmu Talla Duk Da Cewa Aurenta Ya Karato, Cewar Iyayen Yarinyar Da Ta Ajiye Kayan Tallarta Tana Sallah A Bakin Hanya

Daga Abdulmutallib Hamza Kibiya

Alhamdulillah Mun Isa gidan su baiwar Allahn nan Mun Gana da iyayenta, sun Yi mini bayanin cewar yanayin rayuwa yasa ‘yarsu Hauwa’u take zuwa cikin garin Kano tallar Awara daga Bagadawa dake karamar hukumar Dawakin Tofa a nan Kano.

Iyayenta sun yi mana bayanin Yau saura kwanaki 55 aurenta kuma mahaifinta bashi da cikakkiyar lafiya. Sunce Sau 3 Ana Saka aurenta Amman ana dagawa a dalilin rashin wadata da suke chiki.

Bayan Na gayawa iyayenta yau kwana 6 Kenan Muna nemanta Amman bamu same ta ba Sai Yau Allah ya bayyana mana ita Sai mahaifiyarta ta fada mini a Duk tsawon kwana 6 nan tana Azumi ne shiyasa Bata fita talle ba Sai Yau.

Ga wadanda suka bukachi Bata tallafi ga account number Nan zaku Iya Saka abinda Allah ya hore muku.

Allah ya hada mu a ladan, amin.
Domin karin bayani za ku iya kiran wannan lambae;

26-12-2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button