
Innalillahi.. Ku Kalli Bidiyon Jana’izar Mutum 7 Iyalan Gida Daya Da Suka Mutu Bayan Sunci Abinci Mai Dauke Da Guba A Sokoto.
Innalillahiwainnailaihiraju’un Rahotannin da muke samu yanzu yanzu na cewa, wasu yan gida daya sun rasa ransu.

Kamar yadda zaku kalla a bidiyon dake kasa, Mutum 7 iyalan gida guda sun mutu bayan cin abinci mai guba a Sokoto
A Najeriya mutane 7 yan gida guda sun gamu da ajalinsu bayan cin abinci da ake kyautata zaton akwai guba a ciki.
Lamarin dai ya auku ne a kauyen Ƙaura na karamar hukumar Yabo a jihar Sokoto.
Kamar yadda za ku ji a rahoton Faruk Muhammad Yabo mutanen sun hada da Mata 2 na mutum daya da kuma yaransu 5.
Anan Muke Addu’ar Uabangiji Allah Ya Gafarta Musu, Yasa Aljannah Ce Makoma, idan tamu tazo Allah Kasa Mu Cika Da Imani.
Ga Cikakken Rahoton.