News

Bidiyon Ambaliyar Ruwa Da Ta Kashe Mutane Da Dama Tare Da Yin Mummunar Barna A Jahar Plateau

Bidiyon Ambaliyar Ruwa Da Ta Kashe Mutane Da Dama Tare Da Yin Mummunar Barna A Jahar Plateau

Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Tare Da Yin Mummunar Barna A Jihar Filato

Hukumomi a karamar hukumar Pankshin ta Jihar Filato, sun tabbatar da mutuwar mutane hudu, ciki har da wata mace da mijinta, sanadiyyar ambaliyar ruwa da ta auku a kauyukan Nyelleng da Gwabi.

PLATEAU, NIGERIA – Haka kuma a karamar hukumar Quan Pan, ambaliyar ruwa ta shafe gonaki, gidaje da gadoji.

A unguwannin Gangare da Rikkos da ke karamar hukumar Jos ta Arewa ma, ambaliyar ta kwashe gadar da ta hada yankunan biyu, amma tuni shugaban karamar hukumar, Shehu Bala Usman ya sake gina gadar, don hana aukuwar wani ibtila’in.

Tsohon kansila a yankin Nyelleng a karamar hukumar Pankshin, Sudan Bako ya ce karfin ruwa dake saukowa daga tsaunukan dake kewaye da kauyukan, shine ke haddasa ambaliya da lalata gadoji.

Daraktar Hukumar Wayar Da Kan Jama’a Ta Kasa reshen Jihar Filato, Madam Kaneng Pam-Hworo ta ce hukumar na ci gaba da wayar da kan jama’a don su dauki matakan kare kansu daga illar ambaliya.

A Jihar Binuwai ma, fiye da gidaje dari ne ambaliyar ruwa ta shafa, kamar yadda shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar, Emmanuel Shior ya shaida wa manema labarai.

Darakta a ma’aikatar muhalli ta Jahar Filato, Sunda ‘Danbaki ya bukaci jama’a da su rika bin umurnin hukumar yanayi ta kasa.

A kowace shekara dai, Najeriya na asarar makudan kudade, dalilin ambaliyar ruwa, tana kuma shafar lafiyar al’umma da muhalli dake bukatar hukumomi su maida hankali a kai, don rage barnar da ambaliya ke janyowa a kasar.

Ga Karin Bayani

https://youtu.be/KFuP4ZRXnBw

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button