News

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un;! Ƴan Bindiga Sun Sace Mata Da Mijinta A Cikin Garin Katsina

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un;! Ƴan Bindiga Sun Sace Mata Da Mijinta A Cikin Garin Katsina.

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un rahotannin da muke samu yanzu yanzu na cewa,

Ƴan Bindiga Sun Sace Mata Da Mijinta A Cikin Garin Katsina

A Daren Jiya Ƴan Bindiga Suka Kai Hari A Unguwar Shola Dake Bayan Asibitin Koyarwa Ta Gwamnatin Tarayya, Cikin Garin Katsina, Inda Suka Sace Mata Da Mijinta, Matashi Yusuf Bishir Da Matarsa.

Kamar yadda Majiyar RARIYA Ta Nakalto Cewa Sun Kashe Ƴan Banga Biyu Sun Jima Wasu Raunuka a yayin dauki ba dadin.

Jahar katsina dai na cikin jerin jahohin dake fama da hararen yan bindiga makiyaya masu sace mutane dan amsar kudin fansa.

Anan muke addu’ar ubangiji Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukan su.

Ubangiji Allah Ya Kubutar Da Su Cikin Aminci!

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button