News

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un Bidiyon Yadda ambaliyar ruwa ta tayar da ƙauyuka fiye da 100 a Jihar Bauchi

Innalillahi wa inna ilaihi raju’un Bidiyon Yadda ambaliyar ruwa ta tayar da ƙauyuka fiye da 100 a Jihar Bauchi

Ambaliyar ruwa ta tayar da garuruwa da kauyuka fiye da 100 a Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya, a cewar hukumomi.

Kazalika ambaliyar ta haddasa asarar gidaje da dabbobi da kayan amfanin gona da dama a yankin karamar hukumar Zaki ta jihar.

Mutanen da abin ya shafa sun ce an kai masu daukin kwale-kwale na haya, da ke kwashe su daga wuraren da ruwan ya mamaye, amma kuma babu wani tallafi na kayan abinci da magunguna da dai sauransu da suka samu har yanzu.

‘Kaka-ni-ka-yi’
Wani mutum da ambaliyar ruwan ta shafa, wanda kuma shi ne mai garin Dudduru Gasamako, Jauro Musa, ya ce ambaliyar ta ɗaiɗaita su tare da sanya su samu matsugunai a gindin bishiyoyi.

Ya ce wasu mutane sun koma garin Katagum, wasu kuma suna kan Jigawa saboda ambaliyar.

“Ga mu nan cikin gonakin mutane. Ga yara, ga dabbobi, babu abinci, babu komai, abin na tayar da hankali da kuma tausayawa, muna halin kaka-ni-ka-yi,” in ji Jauro Musa.

Ya ce sun yi asarar dabbobi da amfanin gona da kuma gidaje, inda ake tura musu jiragen ruwa domin kwashe su daga wuraren da ambaliyar ta daidaita.

‘Kamuwa da rashin lafiya’
Shi ma wani mutum da ambaliyar ruwan ta shafa da kuma a yanzu yake gudun hijira a garin Zaki, Hassan Wakilin Gasamako, ya ce wasu mutane a wajen da suke hijira na kamuwa da rashin lafiya.

Ya ce mutanen na fama da ciwon ciki da kuma dan zazzabi saboda cizon sauro.

Ya kuma ce akwai wasu mutane da ko tafiya ba su iya yi saboda rashin lafiyar ta yi musu tsanani, inda ya ce suna bukatar kayan agaji da suka hada da kayan abinci da magani da gidajen sauro da tabarmai da kuma abin da za su rufe jikinsu da shi.

Da yake mayar da martani kan bukatar kai musu kayan agaji na gaggawa da mutanen da abin ya shafa suka bukata, darakta mai kula da sashen bayar da taimako da tserar da mutane daga cikin bala’i a hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Bauchi, Bala Yakubu Lame, ya ce yanzu haka gwamnati na shirin kai wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa kayan tallafi da ya hada da kayan abinci da barguna da tabarmai da magunguna da gidajen sauro.

Jami’in ya ce sai nan gaba kadan lokacin da ruwan ya janye, za a samu shiga a duba irin asarar da ambaliyar ruwan ta haddasa.

A bana dai an samu ambaliyar ruwa da dama a jihohin Najeriya ciki kuwa har da Kano da Jigawa da Bauchi da Lagos da sauransu.

Kuma ambaliyar ta haddasa asarar rayuka da dukiya da kuma amfanin gona baya ga rusa gidaje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button