News

Innalillahi: ‘Yan fashin daji sun kashe mutum 18 a Zamfara kuma sun sace gommai a Neja

‘Yan fashin daji sun kashe a ƙalla mutum 18 a wasu hare-hare da suka kai kan wasu ƙauyuka ranar Lahadi, a cewar rahotanni daga jihar Zamfara arewa maso yamma.

A jihar Neja maƙwabtaka ma, mazauna wasu ƙauyuka na ƙaraamar hukumar Rijau na ci gaba da tsere wa gidajensu, bayan wani harin ‘yan fashi, abin da ya kai ga sace kimanin mutum 50.

Wani kansilan mazaɓar Ɗankurmi, Hon Salisu Daraga ya ce maharan sun far wa ƙauyukan Matse-matsi da Katoge da Taɓanni da Matankari, inda suka kashe mutum goma.

“Kawai sai bandit suka fito musu, to a take dai suka kashe mutum goma,” in ji shi.

Wasu ‘yan bijilante a Rijau, sun ce cikin waɗanda ‘yan bindigar suka tafi da su, har da mata da ƙananan yara.

Haka kuma rahotanni na cewa an sace Mallam Abdullahi Zaure, wani dagaci a yankin.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun ya ce jami’ansu na tattara bayanai a kan hare-haren na Rijau, kafin fitar da cikakken ƙarin haske.

Kansilan Ɗankurmi dai ya ce ‘yan fashin sun kuma tare hanyar Ɗankurmi inda suka kashe mutum takwas, waɗanda tuni aka yi jana’izar su a garin Ɗankurmi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button