News

Innalillahi: Mun tsara yadda Tinubu zai janye tallafin fetur – Boss Mustapha

Gwamnatin Najeriya ta ce ta tsara wani kundi da zai taimakawa sabuwar gwamnati ta Bola Tinubu, kan yadda za ta cire tallafin mai ba tare da kalubale ba.

Gwamnatin Buhari ta sanar da cewa ta yi iya kokarinta wajen ganin ta tafiyar da harkokin tallafin mai, duk da dimbin kalubale, sannan ta sanar da kashi tiriliyan 13 daga 2005 zuwa 2021.

A ranar 29 ga watan Mayu ake saran rantsar da Bola Tinubu a Abuja.

Wakilinmu ya rawaito cewa a lokacin wani taro da aka gudanar a Abuja, Sakataren gwamnati Boss Mustapha, ya ce gwamnatin tarayya na bibbiyar abubuwan da ake faɗi kan janye tallafin.

Ya ce daga cikin abubuwan da ake tattauna, shi ne bukatar gyaran matatun man kasar da samar da shirin da zai ragewa mutane radadi tasirin janye tallafin musamman ga talakawa da ma’aikata.

Jaridar ta kuma ambato Boss Mustapha na jadadda cewa suna da kwarin gwiwar sabuwar gwamnati da za a rantsar za ta gudanar da ayyuka da yanke hukunci ba tare da cutar da al’umma ko jefa mutane cikin matsi ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button