News

Video: Yanzu Yanzun Hukumar Yan Sandan Jihar Bauchi Sun Tisa Keyar Dr. Idris Abdulazeez bauchi Zuwa Kurkuku Kuma an hana belin shi

Yanzu Yanzun Hukumar Yan Sandan Jihar Bauchi Sun Tisa Keyar Dr. Idris Abdulazeez bauchi Zuwa Kurkuku Kuma an hana belin shi.

Yanzu Yanzun Hukumar Yan Sandan Jihar Bauchi Sun Kama Malam Idris Abdulazeez Dutsin Tanshi Wanda a kwanakin Baya Yace Bayan buƙatar Taaimakon Mai Daraja Fiyayyen Halitta Annabi Muhd (SAW) Wata Majiya Ta Shaida Mana Cewa an miƙa shi Gidan Yari a Hain Yanzu.

Kamun da akayiwa Malamin Yana da alaƙa da Furucin da yayi a kwanakin Baya na cewar Shi baya Bukatar Taimakon Annabi wanda malamai da dama sukaita cece kuce akai.

Datti Assalfy daya daga cikin masu sharhi akan al’amuran yau da kullum a Shafukan sada Zumunta Shima ya wallafa labarin a Shafin sa na Facebook inda ya wallafa Kamar haka:

HASBUNALLAHU WA NI’IMAL WAKIL.

Ina mai cike da mika dukkan al’amari zuwa ga Allah tare da bakin cikin shaida wa ‘yan uwa Musulmin duniya cewa an gayyaci babban Malamin Addinin Musulunci kuma dodon ‘yan bidi’ah watau Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi, an kaishi Kotu bisa wasu dalilai, yanzu haka yana tsare a kurkuku, Kotu ta hana belin shi.

Muna kira ga ‘yan uwa Musulmi masoya Malam kowa ya kwantar da hankalinsa, sannan a zauna lafiya abi doka, duk abinda ya faru da Malam alheri ne Wallahi, yanzu da’awar tauhidi ta koma kurkuku jami’ar Annabi Yusuf.

Yaa Allah Ka taimaki bawanKa Malam Idris, Ka bashi mafita na alheri Amin.

To Masu sauraron.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button