Kannywood News

Tirqashi: Anya Ali Nuhu Ya Hallaci Makarantar Islamiyya Kuwa? Ina bashi Shawara Ya Koma Makaranta Cewar Ibrahim Mu’azzam

Anya Ali Nuhu Ya Hallaci Makarantar Islamiyya Kuwa? Ina bashi Shawara Ya Koma Makaranta Cewar Ibrahim Mu’azzam.

Kamar dai Yadda aka sani Wakar Wazai baka bayan annabi itace wakar da ta jawo cece kuce a shafukan sada Zumunta inda Malamai da dama sukaita tofa albarkacin bakinsu.

Tun bayan fitowar bidiyon wakar wacce jarumi Ali Nuhu ya hau daga nan ne bidiyon ta kara bayyana a Shafukan sada Zumunta hakan nema yasa dr Idris Abdulazeez bauchi Yayi wata magana wacce itama tabar baya da kura.

Da yawa mutane sun bayyana cewa Kalamar da dr idris din ya fadan akan cewa baya Neman Taimakon annabi sai dai wajen Allah hakan batanci ne ga fiyayyen hallita.

Bayan komai ya lafa sai aka tuntubi jarumi Ali nuhu kan shima ya tofa nasa albarkacin bakin ma’ana yayi karin bayani akan bidiyon wakar daya hau me taken wazai baka bayan Annabi.

A karshe dai Jarumin ya bada tasa fatawar, sai dai wasu malaman sun hango babban kuskure acikin tasa fatawar hakan nema Yasa wani matashin malami a Kafar Sadarwa na TikTok yayi masa martani Sannan kuma ya bashi Shawara cewa Yakamata ya koma Makaranta.

Gadai Cikakkiyar bidiyon nan Kamar haka.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button